Home Labarai Alaafin na Oyo, Oba Lamidi ya rasu

Alaafin na Oyo, Oba Lamidi ya rasu

0
Alaafin na Oyo, Oba Lamidi ya rasu

 

Shahararren masauracin nan, mai rike da sarautar Alaafin a Jihar Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ya mutu.

Ya mutu yana da shekara 83.

Rahotanni sun baiyana cewa ya mutu ne bayan gajeriyar rashin lafiya da tsakar daren Juma’a a Asibitin Horaswa na Afe Babalola a Ado Ekiti.

Gawutaccen masauracin ƙasar yarabawan, wanda ya yi mulki na tsawon shekara 52, shine na uku da ga gidan sarauta na Alowodu.