
Shekara 20 gwamnonin jihar Lagos suka dauka suna kokarin gwamnatin tarayya ta mallaka musu gidan gwamnatin tarayya da aka tashi aka bari, basu samu ba.Ana yi wa gidan lakabi da Marina House, anan gidan Tafawa Balewa da Shehu Shagari suka zauna suka yi mulki. Wato kamar kace Aso Rock na Abuja.
Bola Ahmed Tinubu yana gwamna a 1999 ya nemi Obasanjo ya bashi gidan ya hana. Fashola ya nemi Marigayi Yar Adua da Jonatahan su bashi suka ki. Ana baiwa Fashola ministan ayyuka, da gwamnan Lagos Akinwunmi Ambode ya nema, nan take Buhari ya amince ya mika wa sakataren gwamnatin jihar Lagos Tunji Bello makullan katafaren gidan kyauta, ba diyya , ba ladan ganin ido.
Burin jihar Lagos shi ne ta maida wannan kasaitaccen gini wani hamshakin gidan tarihi kuma cibiya ta duniya ta yawon bude ido domin habaka tattalin arzikinta.
A bara shekarar 2016 shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar kasuwanaci da diflomasiyya kasar China. Kwana shida ya yi cur. A sakamakon wannan ziyarar an kulla yarjejeniyoyi masu dimbin yawa a tsakanin Najeriya da China. Da aka tattara lissafi, kasar China da ‘yan kasuwarata zasu zuba hannun jari a Najeriya na kusan dala biliyan shida, wato naira tiriliyan uku.
A cikin wadannan yarjejejeniya jihar Lagos kadai zata amfana da dala biliyan uku da rabi. Jin dadin yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shige wa Lagos gaba suka samu wannan dama da sarkin Lagos Oba Rilwanu Akiolu da gwamna Ambode sai da suka yi takakkiya zuwa Abuja domin yi wa PMB godiya.
A lokacin da Lagos ta yi bikin cika shekaru 50 da kafawa , Farfesa Osibanjo yana matsayin mukaddashin shugaban kasa, shi ne ya yi wa jihar izinin su fara aikin babban titin International Airport Road zuwa Oshodi. Wannan aikin zai ja kudi kimanin naira biliyan biyar. Abin sha’awa shi ne Osibanjo ya shaida wa Ambode cewa wannan tsaraba ce daga gare shi ta murnar Lagos ta cika hamsin.
Haka zalika, Fashola a matsayinsa na ministan ayyuka ya sanya hannu da Aliko Dangote da wasu yan kasuwa na sake gina titin Wharf Road zuwa Apapa. Tun Fashola yana gwamna yake neman wannan damar bata samu ba, sai yanzu. Titin zai ci naira biliyan hudu da rabi.
Ministan sufuri Rotimi Ameachi kwana hudu da suka gabata ya bayyana cewa an gama duk wani shiri na kammala aikin titi mai tsawon kilomita 150 daga Lagos zuwa Ibadan. Kasar China aka baiwa kwangilar ta dala biliyan daya da rabi. Ana son gama titin a Disamba 2018, a bude shi Janairu 2019.
Filin tashi da saukar jiragen sama na Lagos aka ware domin maida shi matsayi daya da sauran irinsu a duniya. An yi haka ne a shirin maida shi hannun yan kasuwa. Za a kashe kusan naira biliyan 20 a wannan bangaren kawai. Na Abuja ma za a yi masa irin wannan aikin.
Abin lura anan, shi ne Lagos ba da awon igiya ta samu wadannan ayyukan ba. Shiri ne aka yi na zaune ba na tsaye ba.