
Dalibai 47 na Jami’ar Fasaha ta Bells, Ota, Ogun sun kammala karatun digiri da sakamakon ‘1st class’ a shekarar karatu ta 2021/2022.
Shugaban jami’ar, Farfesa Jeremiah Ojediran ne ya bayyana hakan a jiya Asabar, yayin taron bikin yaye ɗalibai na jami’ar, karo na 14, da bayar da shaidar digirin digirgir da kuma raba da kyaututtuka.
A cewar Ojediran, jimillar dalibai 823 ne suka kammala karatu a shekarar karatu ta 2021/2022.
Wannan ya ƙunshi dalibai 47 da suka kammala da sakamakon ‘1st class’, ɗalibai 422 da ke da ‘2nd class’ upper’; 309 sun samu ‘2nd class’ lower’, sannan 45 sun gama a mataki na huɗu wato ‘3rd class’.
Shugaban jami’ar ya ce dalibai 177 da suka kammala karatun gaba da digiri, sun samu sakamako a fannin digiri daban-daban.
Ojediran ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar da kudade yadda ya kamata tare da inganta darajar manyan makarantu da sauran matakan ilimi a kasar nan.
Shugaban jami’ar ya bayyana cewa ilimi na daya daga cikin muhimman abubuwan ci gaban a kasa kuma babu shakka ya zama babban jigon kawo sauyi da ci gaba a tsawon tarihin ɗan adam.