Home Ilimi Ɗaliban firamare miliyan 9.9 mu ke ciyarwa a kullum — Gwamnatin Tarayya

Ɗaliban firamare miliyan 9.9 mu ke ciyarwa a kullum — Gwamnatin Tarayya

0
Ɗaliban firamare miliyan 9.9 mu ke ciyarwa a kullum — Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya, a jiya Laraba ta bayyana cewa a halin yanzu ana ciyar da yara ɗaliban makarantun firamare miliyan 9.9 a duk fadin kasar, a karkashin shirin ciyar da ƴan makaranta, NHGSFP.

Da ta ke jawabi a Akure a lokacin rabon kudade ga talakawa da marasa galihu a jihar Ondo, a karkashin shirin Grant for Vulnerable Groups Programme, GVG, wani bangare na shirin taimakawa masu ƙaramin karfi na kasa, NSIP, Ministar Agaji, Gudanar da Ibtila’i da Ci gaban Jama’a, Sadiya Farouq, ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kara fadada shirin da wasu yara miliyan biyar.

Ministar, wacce ta yi magana ta bakin Daraktan Kudi da Akanta na Ma’aikatar, Matthew Dada, ta ce: “Zan kuma kaddamar da shirin ciyar da makarantu na gida-gida, NHGSFP, wanda ke neman ilimantar da al’umma da masu ruwa da tsaki kan aiwatar da shi ta yadda ya dace da kuma inganci.

“A karkashin NHGSFP, a halin yanzu ana ciyar da yara miliyan 9.9 a duk fadin kasar, kuma Shugaba Buhari ya amince da cewa an fadada shirin da wasu yara miliyan biyar.”

Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, ya ce gwamnatinsa za ta hada kai da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da rayuwa mai kyau ga jama’a.