
Umar Faruq, dalibi ɗan aji 3 da ke karatu a fannin ilimin kimiyyar ɗakin karatu a Jami’ar Bayero Kano, BUK, ne ya lashe zaɓen shugaban Kungiyar Ɗalibai ta Ƙasa, NANS, na 2022 a Abuja.
Faruq ya karɓi kujerar shugabancin an hannun Shugaban NANS mai barin gado, Kwamared Sunday Asefon, wanda aka zaɓa a 2020.
Faruq ya doke abokin hamayyarsa, Kwamared Usman Barambu, inda ya samu kuri’u 202 daga cikin kuri’u 310 da aka kaɗa a zaɓen.
Wakilai sama da 300, da suka haɗa da shugabannin ɗalibai na manyan makarantun ƙasar nan ne su ka hallara a Abuja a ƙarshen mako domin zaɓen sabbin shugabannin da za su tafiyar da harkokin NANS ɗin na tsawon shekara guda.
Sabon zaɓaɓɓen shugaban NANS ɗin, Faruq, wanda ya yi wa manema labarai jawabi jim kaɗan bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen a Abuja, ya sha alwashin ɗaukar matakin gaggawa domin ganin an shawo kan yajin aikin da ƙungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ke yi.
Ya nuna rashin jin daɗinsa kan yajin aikin da malaman makarantar su ke yi, inda ya ce nan take zai gana da ministan ilimi, Malam Adamu Adamu da shugabannin ƙungiyar ASUU da sauran masu ruwa da tsaki kan buƙatar ɓangarori biyun su koma teburin sulhu da nufin warware matsalar, domin ɗalibai su samu su koma ajujuwansu.