
Usman Rimi, ɗalibin da ke shekarar karshe a fannin likitanci da tiyata a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto, UDUS, wanda ya tsunduma harkar sayar da abinci sakamakon yajin aikin ASUU, ya rasu.
Rimi ya bude shagon sayar da abinci da dafa Indomie a yankin Diplomat da ke Sokoto.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya bayar da rahoton cewa ɗalibin ya rasu ne a ranar Laraba bayan gajeriyar rashin lafiya.
Shugaban cibiyar ƴan kasuwa ta 21st Century Entrepreneur Hub, Umar Idris, na kusa da marigayin, shi ne ya tabbatar wa NAN rasuwar a yau Asabar.
Idris ya ce an yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garinsu, Rimi da ke Ƙaramar Hukumar Rimi a jihar Katsina.
Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai tawali’u kuma dalibi mai kwazo kuma dan kasuwa.