Home Labarai Ɗalibin da yai suka ga Aisha Buhari ya bata hakuri bayan ta janye ƙarar da ta kai shi

Ɗalibin da yai suka ga Aisha Buhari ya bata hakuri bayan ta janye ƙarar da ta kai shi

0
Ɗalibin da yai suka ga Aisha Buhari ya bata hakuri bayan ta janye ƙarar da ta kai shi

Bayan sakin sa daga gidan yari, dalibin shekarar karshe a jami’ar tarayya da ke Dutse, Aminu Mohammed, ya nemi gafarar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, bisa laifin da ya yi mata.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan ya isa makarantar a daren ranar Asabar, Mohammed ya nuna nadama kan sukar da ya wallafa a kan uwargidan shugaban kasar a shafinsa na Twitter, inda ya ce zai canza halin sa.

“ina mai amfani da wannan kafar wajen bada hakuri ga wadanda na ɓata wa, musamman uwar mu, Aisha Buhari. Ba Ni da niyyar cin mutuncin ki, kuma insha Allahu zan canza halaye na. Ina kuma godiya da yafe min da ki ka yi, na gode mama.

“Zan kuma so in yi amfani da wannan kafar domin nuna godiya ta ga wadanda su ka goya min ba lokacin da na na shiga cikin yanayi mafi kunci a rayuwa ta, mutum ba zai iya kubuta daga kaddararsa ba amma abin da ya faru ya zama darasi ga dukkanmu. Na gode duka da ƙauna,” in ji shi

A tuna cewa an dai cafke Aminu ne bayan ya wallafa wasu kalamai na suka ga Aisha Buhari, inda a ka kama shi har zuwa ga gidan yari.