
Alkalin Alkalan na Ƙasa, CJN, Mai Shari’a Muhammad Tanko ya yi murabus daga mukaminsa, bisa dalilai na lafiya.
Mataimaki na musamman ga CJN kan harkokin yaɗa labarai, Isah Ahuraka ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN
Mai shari’a Olukayode Ariwoola ne mafi girman muƙami bayan mai shari’a Mary Odili ta yi ritaya a ranar 12 ga watan Mayu bayan ta kai shekaru 70 da haihuwa.
An haifi Mai shari’a Tanko a ranar 31 ga Disamba, 1953.
Ya fito daga Doguwa, Ƙaramar Hukumar Giade ta Jihar Bauchi.