
Mataimakin Kwamanda-Janar na Hisbah a Jihar Kano, Mallam Yakubu Maigida Kachako ya baiyana cewa aljanu sun koma kan TikTok domin su ci gaba da shiga jikin shagalallun mata.
A wata hira da manema labarai a Kano a ranar Talata, Kachako ya baiyana cewa su aljanu su na son tarewa a inda mata su ke taruwa domin su shiga jikinsu su illata su.
Ya ƙara da cewa a da, aljanu a makarantun ƴan mata, musamman makarantun kwana su ke taruwa, da ga bisani sai su ka koma gidajen biki da walima.
Kachako, wanda masani ne a kan harkar aljanu ya baiyana cewa, sakamakon riƙon da ƴan mata su ka yi wa sabuwar hanyar sadarwar nan ta TikTok, sai aljanu su ka koma can domin su ci gaba da shiga jikin ƴan matan.
Ya ƙara da cewa mata masu yin TikTok su lura za su riƙa ganin wasu baƙin fuskoki a Tiktok, in da ya tabbatar da cewa waɗannan baƙin fuskokin to aljanu ne.
“Aljanu sun koma tiktok. Da a makarantun kwana da na jeka-ka-dawo a ke samun aljanu. Da ga bisani sai su ka koma gidajen biki. To yanzu sun bar gidajen biki. Idan an tashi daga biki ko gurin walima sai su bi mata gida su shiga jikin su.
“Yanzu kuwa da masu yin TikTok sun lura, za su ga wasu bakin fiskoki, to waɗan nan fuskokin aljanu ne. Suma yanzu sun koma tiktok ana damawa da su. Sabo da haka mata sai a yi hattara,” in ji Kachako.