
Babbar kotun tsarin Mulki ta kasar Austeriya ta cimma matsaya kan halatta auren tsakanin ‘yan Luwaɗi da Maɗigo. Amma wannan damar zata fara ne daga farkon Shekarar 2019, a cewar kotun, dokokin baya da suka yi hani ga auren jinsi sun yi tsauri.
Wannan al’amari ya sanya kasar Austeriya tabi sahun manyan kasashen Turai da suka yi amanna da halatta aure tsakanin ‘yan Luwaɗi da Maɗigo, irinsu Faransa da Jamus da Sifaniya da kuma Burtaniya.
A baya dai, dokokin kasar Austeriya, sun amince a kulla soyayya tsakanin Namiji da namiji ko Mace da Mace, amma basu amince a yi aure ba, sai a 2010 aka fara kiraye kirayen bayar da iznin ɗaura auren ‘yan Luwaɗi da Maɗigo.
A shekarar 2009 wasu budurwoyi guda biyu, suka nemi wata kotu a birnin Biyana, da ta basu iznin yin aure tsakaninsu, abinda kotun ta ce sam ba zata sabu ba. Tun wancan lokaci ne, kungiyoyin kare ‘yancin bani adamasukai ta kururuwar an dannewa wadannan ‘yan mata hakkinsu na zabin abinda suke so.
Jaridun ranar Talata na kasar Austeriya, sun buga labarin cewar, hanin da aka sanya kan auren jinsi zai zo karshe nan da Shekarar 2019, inda doka zata baiwa samari da ‘yan mata kulla aure a tsakanin jinsinansu.
Tuni dai kungioyin ‘yan Luwadi da na madigo suka dinga sowwa kan tituna suna murna da samun janye wannan dokar da suka kira Alakakai, wadda ta hana musu bin tsarin rayuwar da suka zabarwa kansu.
Luwadi dai na daga cikin manyan laifuka a cikin Addinin Musulunci, haka kuma, dokokin addinin Islama sun hana duk wani abu da zai kai ga samun auratayya tsakanin jinsi guda.