
Wani magajin-gari a Mexico ya auri wata kada sanye da rigar aure, inda a ka ɗaura auren ta hanyar sumbatar dabbar.
Aure na daga cikin tsohuwar al’adar ƴan asalin ƙasar, wanda magajin garin, Victor Hugo Sosa ya jagoranta, kuma ya yi niyya don kawo wadata a ƙauyen San Pedro Huamelula a kudu maso yammacin Mexico.
Ita wannan dabba mai rarrafe, mai shekaru bakwai haihuwa, sananna ce a garin, inda a ka laƙaba mata suna da ƴar ƙaramar gimbiya, inda kuma a ke mata kallon abar bauta kuma uwa ma bada mama.
Auren da ta yi ga magajin gari yana nuna cewa ta shigo cikin bani-adam.
Bikin ya kayatar, in da a ka yi kade-kade da wake-wake na gargajiya da raye-raye, yayin da ake kira ga magajin garin da ya sumbaci sabuwar amaryarsa.
An buƙaci ango da ya sumbaci amaryarsa.
An yi ta kaɗa ganguna a lokacin da mai-garin ya dauki amaryarsa kada a hannunsa a kan tituna yayin da maza ke ta murna da jefa huluna sama.
Elia Edith Aguilar, wadda aka fi sani da uwargidan da ta shirya bikin auren, ta ce: “na samu farin ciki sosai kuma na yi alfahari da tushena.
Al’ada ce mai kyau sosai.”
Ta kara da cewa babban gata ne a amince da gudanar da bikin.
An daure bakin kadar don gujewa cizo, yayin da magajin-gari ya sumbace ta sau da yawa a yayin bikin.