
Sanata Abdullahi Adamu, sabon shugaban jami’yar APC a yau Laraba ya baiyana cewa Allah ne Ya zaɓe shi ya zama shugaban jami’yar a babban taron da a ka yi ranar 26 ga watan Maris.
Adamu ya fadi hakan ne a sakateriyar APC a Abuja jim kaɗan bayan ya karbi tutar kama aiki a hannun tsohon shugaban rikon jam’iyar, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni.
“Allah Ya zaɓe mu mu ka zama ƴan kwamitin zartaswa na jam’iyar mu mai albarka.
“A haka za a ga kamar abu ne mai sauki, to ba yin mu ba ne kawai yin Allah ne. Shi ya ke yin yadda Ya so.
“Wata ɗaya da ya wuce nan zaci zan zama shugaban jami’ya na ƙasa ba, amma gashi yau gashi ina karbar sandan mulki da ga ha bin tsohon shugaban riƙon jam’iyar.
“Allah ne kawai zai iya yin haka. Ba wai Hikima ta da martaba ta ce ta kawo ninkujerar nan ta hisba, za a iya samun alamomin hakan,”