Home Labarai Amarya ta yanke wa angonta mazakuta a Katsina

Amarya ta yanke wa angonta mazakuta a Katsina

0
Amarya ta yanke wa angonta mazakuta a Katsina

Rundunar ƴansanda a jihar Katsina, ta tabbatar da cafke wata amarya mai suna Tinene Isa, bisa zargin yanke mazakutar angonta.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansandan, ASP Abubakar Aliyu ne ya tabbatar da kamen a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a yau Laraba a Katsina.

Ya ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Kafur.

Aliyu, wanda bai bayyana sunan wanda ibtila’in ya afku a kansa ba, ya ce yana cikin mawuyacin hali inda ake kula da lafiyarsa a babban asibitin Malumfashi.

Ya ce wacce ake zargin ta yi amfani da reza wajen aikata laifin.

“Na gaya muku, muna gudanar da bincike kan lamarin.

“Amarya ce, ta haura shekara 30, watakila ta dauki lokaci mai tsawo kafin ta yi aure, ko kuma ba aurenta ne na fari ba.

“Ba ni da cikakken bayani, za mu gano duk wadannan a bincikenmu,” in ji shi.

Ya ce za a gurfanar da wacce ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.