
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce ya shiga damuwa kan yiwuwar wasu kwamandojin Boko Haram sun tsere daga gidan gyaran hali na jihar sakamakon ambaliyar ruwa da ta afkawa garin Maiduguri.
Ambaliyar ruwan dai ta jawo asarar rayuka da dukiyoyi a jihar.
Acewar rahotanni, ambaliyar ruwan ta lalata wani bangare na tsohon gidan bursin inda aka debe daurarru da dama zuwa sabon gidan bursin matsakaici a Maiduguri.
Wata majiyar tsaro ta tabbatar da hakan ga wakilin Daily Trust.
Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba, sun ce yayin da aka kwashe wasu daga gidan kurkukun, wasu kuwa sun tsere.
Yayin da aka tambaye shi, ko yana damuwa kan cewa wasu shugabannin Boko Haram ka iya tserewa, sai Gwamnan Zulum ya mayar da amsa da cewa ya damu.
Ya ce, “Ina damuwa, eh, ina damuwa matuka. Amma ya kamata kasa a ran ka cewa gwamnatin jihar Borno ta kafa inda ‘yan tada kayar baya zasu tuba. Shekaru 2 da suka gabata, Mayakan Boko Haram da iyalansa 200, 000 suka tuba, kuma ina tunanin hakan yana haifar da sakamako mai kyau wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali”
Zulum ya kuma koka kan yadda jihar ta sake samun kanta cikin annoba a yayin da take fuskantar matsalar tsaro.
“Zan iya tunawa, an kashe sama da mutane dubu 300, an lalata dubban ajujuwa na karatu, ‘yan tada kayar baya sun lalata daruruwan wurare.
” Muna ta kokarin fita daga wannan matsalar, yanzu kuma ga wani bala’in”.