
Ambaliyar ruwa da ta afkawa birnin Maiduguri na jihar Borno ta jawo asarar rayuka 30, inji hukumomi a jiya Laraba.
Daruruwan gidaje ne ambaliyar ta tafi dasu, wacce kuma ta yi barna a gonaki da unguwanni da wuraren kasuwanci.
Ambaliyar ta faru ne bayan ballewar Dam din Alau dake garin Maiduguri.
“Adadin mutanen da suka mutu sun kai 30”, inji mai magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA, Ezekiel Manzo.
Kodayake, mazauna garin sun ce adadin wadanda suka rasu ka iya fin haka saboda har yanzu akwai mutane ciki har da kananan yara da ba a gansu ba.
“Babu wani da yasan adadin mutanen da suka mutu sakamakon wannan iftila’i”, inji Tasiu Abdullahi, mazaunin yankin Gwange da lamarin ya shafa.
” Zasu iya kai 60 ko fiye da haka”, inji wani direban Taxi, Babagana Modu.
Wuraren da ambaliyar tafi shafa sun hada da: Kasuwar Monday Market da fadar Shehun Borno da Shehuri da Gwange da Adamkolo da Gamboru da Fori da Bulabulin da Moromoro da gadar Kwastom.
Ambaliyar ta tafiyar da makabartar Gwange inda ake ganin gawarwaki na yawo cikin ruwa a kan hanya.
Marasa lafiya a asibitin koyarwa na Maiduguri ma abin ya shafe su.
Gwamna, Babagana Zulum na jihar Borno ya ce ambaliyar ta shafi a kalla mutane Miliyan 1.