Home Labarai Ambaliya: Sama da mutane 200,000 sun rasa mahallai inda yara da dama su ka ɓace a Maiduguri

Ambaliya: Sama da mutane 200,000 sun rasa mahallai inda yara da dama su ka ɓace a Maiduguri

0
Ambaliya: Sama da mutane 200,000 sun rasa mahallai inda yara da dama su ka ɓace a Maiduguri

Ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da sanyin safiyar jiya, ta mamaye daruruwan gidaje tare da lalata dimbin dukiya.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta tabbatar da cewa sama da mutane 200,000 ne suka rasa muhallansu.

NEMA ta ce mutane da ƙananan yara da ba a san adadin su ba sun ɓace, inda ta tabbatar da cewa ambaliyar ta lalata kadarori da dama da suka hada da, gidaje, gonaki da wuraren kasuwanci.

Mazauna garin, wadanda akasarin su ‘yan karamar hukumar Jere ne, an tilasta musu barin gidajensu.

Ambaliyar ruwan ta biyo bayan rugujewar madatsar ruwa ta Alau, wadda daga kimanin kilomita 10 zuwa cikin babban birnin jihar.

Matsuguni da wuraren kasuwanci sun nutse cikin ruwa da suka hada da shahararriyar Kasuwar Monday da dubban gidaje da kadarori, kamar fadar Shehun Borno, Shehuri, Gwange, Adamkolo, Gamboru, Fori, Bulabulin, unguwannin gidan waya, Moromoro, da kwastam. Gadar da dai sauran su ma abin ya shafa.

Yawancin mazauna garin da suka zanta da Daily Trust sun ce ba su iya gano ‘yan uwansu ba a halin yanzu.