
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauka a birnin Maiduguri na jihar Borno domin jajanta wa al’ummar jihar bisa ibtila’in ambaliyar ruwa da ta samu garin.
A jiya ne dai Tinubu ya dawo daga tafiya, inda ya je China da Burtaniya.
Tun ya na can ya umurci mataimakin sa Kashim Shettima da ya ziyarci Maiduguri ya ga abinda ke faruwa.
Sai shi ma Shugaban ya tashi kafa da kafa zuwa Maiduguri, inda ya sauka da misalin ƙarfe 3:20 na rana.