
Majalisar zartaswa ta jihar Kano ta amince, tare da ba da umarnin rushe duk wasu gine-gine da aka yi a kasuwar Kantin Kwari, musamman waɗanda a ka yi a kan babbar kwatar nan ta Kwarin Gogau.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke bayyana wa manema labarai sakamakon taron majalisar zartarwas na mako-mako, wanda aka gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnatin Kano a jiya Laraba.
An bada umarnin rushe duk gine-ginen dake kan magudanun ruwa a ciki da kewayen kasuwar da nufin kawar da duk wani abun da ke kawo cikas ga ruwan dake wucewa ta cikin kasuwar har ya haifar da ambaliya.
Bayan karɓar rahotannin abubuwan da suka haifar da ambaliyar ruwa a kasuwar daga kwamishinnan ayyuka Injiniya Idris Wada Saleh da na Muhalli, Dokta Kabiru Ibrahim Getso, majalisar ta kuma ba da umarnin a rushe duk wasu gine-gine na wucin-gadi da aka yi a hanyar ruwa dake ciki da wajen kasuwar nan take.