Home Labarai Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 3 da lalata gidaje 1,453 a Bauchi

Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 3 da lalata gidaje 1,453 a Bauchi

0
Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 3 da lalata gidaje 1,453 a Bauchi

 

Babban Daraktan Hukumar kare Muhalli ta Jihar Bauchi, BASEPA, Ibrahim Kabir ya tabbatar da mutuwar mutane 3 sakamakon ambaliyar ruwa da ta lalata gidaje 1,453 da gonaki da dama a Kananan Hukumomin Zaki da Gamawa.

Kabir ya bayyana haka ne a lokacin da yake shaida wa Gwamna Bala Mohammed, lokacin da ya kai ziyarar jajantawa al’ummar da abin ya shafa a jiya Asabar, a Ƙaramar Hukumar Zaki.

Ya ce bayan tantance irin ɓarnar da mamakon ruwan sama ya yi a ranar Laraba, an gano ya kashe mutane 3 da lalata gidaje 1,453 da gonakin da ba a tantance adadinsu ba a kananan hukumomin biyu.

Ya ce ambaliyar ta kuma katse hanyoyin da suka haɗa ƙananan hukumomin biyu da al’umma da kuma wasu sassan jihar a wurare 6 a kan babbar hanyar.

“A matsayin matakan gaggawa, al’ummomin na buƙatar kwale-kwale 14 a matsayin hanyar sufuri don ketare hanyoyin da aka yanke don ci gaba da kasuwancinsu na yau da kullum,” in ji shi.

Kabir ya shawarci al’ummomin da su kaura zuwa wuraren da babu ambaliyar domin tabbatar da tsaron lafiyarsu.

Gwamnan ya jajanta wa al’ummar yankin kan mutuwar mutane uku da lalata gidaje da gonaki a kananan hukumomin Zaki da Gamawa.

Ya yi kira da a haɗa karfi da karfe wajen magance munanan illolin da ambaliyar ruwa ta addabi al’umma a fadin jihar.