
Ambaliyar ruwa ta baya-bayan nan ta kashe akalla mutane 50 a ƙauyuka 11 a Adamawa tare da jikkata wasu 71.
Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa, ADSEMA, Suleiman Mohammed, ne ya bayyana hakan a yau Juma’a a Yola lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN.
Ya ɗora laifin ambaliyar a kan sako ruwa daga Dam ɗin Lagdo da ke makwabtaka da Kamaru.
Mohammed ya kuma ce ambaliyar ta lalata gonaki 172,000 da kayayyakin abinci na miliyoyin naira.
“Wasu daga cikin kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Numan, Shelleng, Yola South, Yola North, Demsa, Mayo Belwa da Michika,” in ji shi.
Ya kara da cewa hukumar ta samar da kayan sawa, kayan abinci, magunguna, gidajen sauro, barguna da bokitai ga wadanda abin ya shafa domin rage musu radadi.
“Gwamnatin Jiha, Gwamnatin Tarayya da sauran masu hannu da shuni ne suka bayar da kayayyakin,” inji shi.
Mohammed ya kuma shaida cewa ADSEMA za ta hada kai da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA, domin kai al’ummomin da abin ya shafa zuwa wurare masu tsaro.
“Za mu ci gaba da wayar da kan al’umma game da hadarin da ke tattare da zama a yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa,” in ji shi.