
Gwamnatin tarayya, a yau Talata ta bayyana cewa mutane 500 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a fadin kasar.
Ta ce kawo yanzu ambaliyar ta yi barna a Jihohi 31 na tarayya da kuma Abuja, inda lamarin ya shafi sama da mutane miliyan 1.4 a faɗin ƙasar nan.
Gwamnatin Tarayya ta kuma ce gonaki da gidaje da dama sun lalace sakamakon illar da ambaliyar ta yi.
Sai dai gwamnatin ta ce ya yi wuri a fara kimanta asarar da lamarin ya haifar tunda har ya zu ana ci gaba da ganin illar.
Babban Sakatare na dindindin na Ma’aikatar Agaji, Magance Bala’i da Cigaban Jama’a, Dakta Nasir Sani Gwarzo ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke bayar da bayanai kan ambaliyar ruwa da ta afku a baya-bayan nan.
Ya ce daftarin da hukumar ta FEC ta amince da shi na tunkarar matsalar ambaliyar ruwa da ta afku a Najeriya kwanan nan, zai jagoranci masu ruwa da tsaki wajen dakile illar ambaliyar.
Ya ce: “Sama da mutane 500 ne aka ruwaito sun mutu. Mutane 1,411,051 abin ya shafa. ‘Yan gudun hijirar da suka kaura daga inda suke sun kai 790,254.
“Kusan mutane 1,546 da suka rasa matsugunansu sun samu raunuka.
“Bugu da kari, gidaje 44,099 sun lalace; Gidaje 45,249 sun lalace gaba daya sannan kadada 76,168 na gonaki sun lalace yayin da kadada 70,566 na gonaki suka lalace gaba daya sakamakon ruwan sama.”
Dangane da kokarin da aka yi na dakile tasirin, ya ce: “A wannan matakin, muna daukar dukkan matakan da suka dace don kawo dauki ga mutanen da abin ya shafa.