
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta gargaɗi ƴan Nijeriya kan illar bleaching .
Darakta-Janar ta NDLEA, Mojisola Adeyeye, a cewar wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, ta hannun mai ba da shawara kan harkokin yada labarai, Olusayo Akintola, ta yi wannan kiran a wani taron manyan jami’an hukumar a Legas.
Ta nanata cewa yin amfani da kayan kwalliya na iya haifar da lahani ga sassan jiki da kuma haifar da mutuwa.
Adeyeye ta bayyana kaduwarta game da haɗawa tare da yin amfani da sinadarai marasa rijista ga al’umma.
Shugaban NAFDAC ta ce: “Ba wai kawai muna haramta kayayyakin ne saboda suna yin bleaching ba, an hana su saboda matsalolin da ke tattare da wasu sinadaran da ke cikin kayayyakin hadawar.
” Yawancin waɗannan samfuran na iya haifar da ciwon daji na fata tare da lalata hanta da koda.
“ hasken fata a yau na iya zama cutar kansa gobe, da yawa daga cikin masu shigo da kaya suna shigo da kayayyakin zuwa cikin kasar nan da sunan jerin sunayen duniya don kaucewa binciken hukumar NAFDAC.
”Bleaching ya zama annoba a tsakanin mata da takwarorinsu maza. Hukumar tana bin diddigin wasu mutanen da suka tsunduma cikin siyar da kayan kwalliyar da ba su izini ba a intanet.
“An baiwa hukumar bincike da tilastawa ta NAFDAC umarnin damke masu sayar da wadannan kayayyaki masu hatsarin gaske tare da gurfanar da su gaban kotu.” In ji ta.
Ta jaddada cewa hukumar ba ta adawa da amfani da kayan kwalliya ba, amma dole ne a daidaita su tare da tabbatar da lafiyar dan adam.