Home Labarai Ba za mu amince da yunƙurin juyin-mulki a Nijar ba — Tinubu

Ba za mu amince da yunƙurin juyin-mulki a Nijar ba — Tinubu

0
Ba za mu amince da yunƙurin juyin-mulki a Nijar ba — Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, yunkurin juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar a safiyar ranar Litinin da wasu sojoji da har yanzu ba a kai ga gano su ba su ka yi.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba a Abuja, Tinubu ya ce shugabannin ECOWAS ba za su lamunta da duk wani yanayi da zai kawo cikas ga gwamnatin da aka zaba ta hanyar dimokradiyya ba.

‘’Bayanai da mu ke samu daga jamhuriyar Nijar na nuni da wasu abubuwa marasa dadi da ke tattare da manyan shugabannin siyasar kasar.

Ya kamata a fayyace ga dukkan ƴan jamhuriyar Nijar cewa shugabannin yankin ECOWAS da duk masu son dimokuradiyya a duniya ba za su amince da duk wani yanayi da zai kawo cikas ga gwamnatin da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya a kasar ba.

‘’Shugabannin ECOWAS ba za su amince da duk wani mataki da zai kawo cikas ga gudanar da halaltacciyar gwamnati a Nijar ko wani yanki na yammacin Afirka ba.

“Ina so in ce muna sa ido sosai kan al’amura da abubuwan da ke faruwa a Nijar kuma za mu yi duk abin da za mu iya don tabbatar da cewa dimokuradiyya ta kafu, ta bunkasa, da tushe mai kyau a yankinmu,” in ji Tinubu.