Home Labarai Amurka ta yi alƙawarin taimaka wa Nijeriya a yaƙi da ta’addanci da samun sahihin zaɓe a 2023

Amurka ta yi alƙawarin taimaka wa Nijeriya a yaƙi da ta’addanci da samun sahihin zaɓe a 2023

0
Amurka ta yi alƙawarin taimaka wa Nijeriya a yaƙi da ta’addanci da samun sahihin zaɓe a 2023

 

 

Amurka ta jaddada aniyarta ta yaƙi da ta’addanci a Najeriya, da kuma tabbatar da an yi sahihin zaɓe a 2023.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ne ya bayar da wannan tabbacin a cikin wata sanarwa da ya fitar ta taya Nijeriya bikin cikar shekaru 62 da samun ƴancin kai.

Blinken ya lura cewa, Amurka ta na kuma da burin a gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci a kasar a shekara mai zuwa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A madadin kasar Amurka, ina mika sakon fatan alheri ga al’ummar Najeriya kan bikin cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai.

“Hadin gwiwar da ke tsakanin kasashenmu biyu na da karfi kuma an gina ta ne bisa ka’idojin dimokuradiyya, da alakar kasuwanci.

“Amurka ta kuduri aniyar tallafa wa kokarin Najeriya na yaki da ta’addanci da rashin tsaro, inganta tsarin kiwon lafiya, karfafa cibiyoyin dimokiradiyya, inganta mutunta hakkin dan adam, da karfafa ci gaban tattalin arziki ciki har da kasuwanci da saka hannun jari tsakanin Amurka da Najeriya.

“Mun tsaya tare da Najeriya a matsayin abokiyar kawancen dimokaradiyya wajen tallafa wa zaɓuka a yi su cikin gaskiya da adalci da kuma martaba shugabancin Najeriya kan al’amuran duniya da na shiyya-shiyya ciki har da yaki da annobar COVID-19,” in ji shi.