
Amurka ta sake umartar ƴan ƙasarta da su yi maza su bar Ukraine yayin da kasar ke fuskantar barazanar hare-hare da ga sojojin Russia, kamar yadda fadar Shugaban Ƙasar Amurkan ta ba da shawara.
“Ka da wanda ya je Ukraine saboda barazanar da sojojin Russia ke yi da kuma cutar korona, sannan waɗanda su ke cikin Ukraine ɗin ma su fice yanzu-yanzu ta ababan hawa na haya ko ba na haya ba.
“Waɗanda kuma za su ci gaba da zama a Ukraine to su zamo sun kiyaye sabo da laifuka da ke ƙaruwa da kuma barazanar hare-hare da ga sojojin Russia,” in ji sanarwar.
A ranar 23 ga watan Janairu ne Amurka ta bada izinin kwashe iyalan ma’aikatan diflomasiyya ɗin kasar da kuma ma’aikata da ga Ukraine.
Haka kuma Amurka ta shawarci ƴan kasar mazauna Ukraine da su yi gaggawar ficewa saboda rashin tabbas da zaman ɗar-ɗar da ya ke afkuwa a Ukraine ɗin.