Home Ƙasashen waje Amurkawa na sayen galan ɗin fetur kimanin naira 3000 a kuɗin Nijeriya

Amurkawa na sayen galan ɗin fetur kimanin naira 3000 a kuɗin Nijeriya

0
Amurkawa na sayen galan ɗin fetur kimanin naira 3000 a kuɗin Nijeriya

 

 

 

Masu motoci a Amurka na shan baƙar wuya a faɗin Amurka inda suke biyan aƙalla dala biyar kimanin naira dubu uku domin sayan galan ɗaya na fetur.

Wannan ne karon farko da irin wannan lamari ke faruwa a Amurka. A wasu jihohi na ƙasar kamar irin su California, farashin ya ɗara haka.

Shugaba Biden na Amurka ya yi ƙoƙarin bayar da umarnin amfani da man fetur ɗin Amurka da aka tanada domin ko ta kwana don rage farashin man.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke ƙoƙarin shawo kan matsalar tashin farashin kayayyaki a ƙasar wanda rabon da a samu irin haka kusan shekara 40.

Ƙarin farashin fetur ya samo asali ne sakamakon rage adadin man da ake tacewa sakamakon korona da kuma takunkumin da aka saka wa Rasha, wadda tana daga cikin manyan ƙasashen da suka fi samar da man fetur a duniya.