
A wata sanarwa da kungiyar Malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta fitar a shafinta na Twitter ta bayyana cewar sun cimma yarjejeniya tsakaninta da Gwamnatin tarayya.
Haka kuma, kungiyar ta bayyana cewar suna duba yuwuwar janye yajin aikin da suka shafe kwanaki suna yi.