
Ana kyautata zaton an kashe matafiya da dama kuma an yi garkuwa da wasu da dama bayan da ƴan ta’adda su ka buɗe musu wuta a kan hanyar Kaduna-Zariya wacce ba ta rabuwa da motoci a ko da yaushe.
Harin ya faru ne a daidai Ƙofar Gayan, da misalin ƙarfe 8 na dare, bayan da ƴan ta’addan su ka fara harbi kan-mai-uwa-da-wabi domin su datse matafiyan su kuma yi awon-gaba da su.
Shaidun gani da ido sun shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN cewa ƴan ta’addan sun yi awon-gaba da matafiya da dama cikin jeji kafin jami’an tsaro su zo wajen.
“Sun yi garkuwa da matafiya da dama. Wasu dai sun tsere amma sun kashe da dama. Ba za mu iya ƙaiyade adadin waɗanda a ka kashe da sacewa ba,” in ji wani wanda lamarin ya faru a idonsa.
Wani shaida ma ya ƙara da cewa an hallaka wani Sani Dogara a harin.
Har yanzu dai Rundunar Ƴan Sanda ba ta ce komai ba.
.