Home Labarai Ana samun ɓullar Omicron a Nijeriya, Shugaban Ƙasar Afirka ta Kudu ya bazamo zuwa Nijeriya

Ana samun ɓullar Omicron a Nijeriya, Shugaban Ƙasar Afirka ta Kudu ya bazamo zuwa Nijeriya

0
Ana samun ɓullar Omicron a Nijeriya, Shugaban Ƙasar Afirka ta Kudu ya bazamo zuwa Nijeriya

 

Yayin da ƙasar Nijeriya ta shiga fargabar ɓullar hatsabibin nau’in cutar koronan nan da a ka yiwa laƙabi da Omicron, kwatsam sai ga Shugaban Ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya bazamo zuwa ƙasar nan.

Bayan da Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa an samu mutane 2 ɗauke da sabon nau’in koronan a ƙasar nan, ba a daɗe ba sai a ka ƙara samun wani ɗauke da ita, duk a yau Laraba.

Da ma ita wannan Omicron ɗin dai ta samo asali ne daga Afirka ta Kudu, kuma bincike ya nuna cewa waɗan nan masu ɗauke da ita a ƙasar nan ɗin daga kasar su ka shigo Nijeriya.

Ai kuwa sai ga shuganan ƙasar ta Afirka ta Kudu, Ramaphosa ya falfalo wajen Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Shi kuwa Buhari, Ramaphosa ya na isowa da misalin ƙarfe 10 na safe, sai ya sa a ka buga masa fareti sannan a ka harba bindigar ban-girma sau 21.

A na tunanin ya zo ƙasar nan ne domin su tattauna da shugaba Buhari a kan yadda za a haɗa karfi waje guda domin a shawo kan lamarin.