Home Siyasa ANA WATA GA WATA: Har yanzu nine ɗan takarar gwamna na ADP ba Sha’aban Sharada ba — Koguna

ANA WATA GA WATA: Har yanzu nine ɗan takarar gwamna na ADP ba Sha’aban Sharada ba — Koguna

0
ANA WATA GA WATA: Har yanzu nine ɗan takarar gwamna na ADP ba Sha’aban Sharada ba — Koguna

 

 

 

Wani ɗan siyasa a Kano, Nasiru Koguna, ya kafe kai da fata ya na ikirarin cewa har yanzu shi ne ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADP, a Kano, ba Sha’aban Sharada ba.

Daily Nigerian Hausa ta rswaito cewa a makon da ya gabata ne Sharada ya sanar da ficewar sa da ga APC zuwa ADP, har ma ya samu tikitin takarar gwamna a Kano.

Sai dai kuma a wata wasika da ya aike wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Koguna, ta hannun lauyansa Farfesa Nasiru Aliyu, SAN, ya ce shi ne wanda wakilan jam’iyya su ka zaba bisa ka’ida a matsayin dan takarar ADP.

Ya kara da cewa shi da kansa bai rubuta wa hukumar zabe ta INEC sanarwar janyewa ba kamar yadda dokar zabe ta 2022 ta tanada.

Wasikar ta kara bayyana yadda shugaban jam’iyyar na kasa ya kirkiro da hanyar sauya sunan Koguna ɗin ba tare da bin ka’ida ba kamar yadda doka ta tanada.

A wasiƙar, lauyan na Koguna ya kuma bayyana cewa an yi masa romon baka, inda uwar jam’iyyar ta nuna cewa ya amince da sauya shi da Sharada, ta hanyar rubuta wa INEC, sannan duk abin da ya kashe za a mayar masa.

“Amma abin takaici, sai kawai mu ka ji wai an yi wani ƙwarya-ƙwaryan zaɓen fidda-gwani wai an maye gurbin Koguna da Sharada ba tare da shi Koguna ya rubuta wa INEC da cike fom ɗin janye wa ba na kashin kan sa.

“Dalilin haka ne ya sa mu ka rubuta muku cewa wanda mu ke karewa har yanzu shi ne ɗan takara na jam’iyar ADP,” in ji lauyan.