Home Labarai Zaɓen ƙananan hukumomi a Kano: Gwaji ya nuna ƴan takara 20 na shaye-shaye – NDLEA

Zaɓen ƙananan hukumomi a Kano: Gwaji ya nuna ƴan takara 20 na shaye-shaye – NDLEA

0
Zaɓen ƙananan hukumomi a Kano: Gwaji ya nuna ƴan takara 20 na shaye-shaye – NDLEA

A kalla ƴan takara 20 a zaben kananan hukumomi dake tafe a jihar Kano a ka samu suna shaye-shaye a gwajin da hukumar NDLEA ta yi musu.

Kwamandan hukumar ta NDLEA na Kano, Abubakar Idris Ahmad ne ya tabbatar da hakan ga jaridar Daily Trust a ofishin sa.

Ya ce, wasu daga cikin ƴan takarar, gwaji ya nuna suna shan codeine da ganyen wiwi.

“Masu neman takara 20 da jam’iyyar NNPP ta gabatar mana, gwaji ya nuna suna shan muggan kwayoyi kuma ana ci gaba da gwajin.”

Sai dai ya ce babu mace a masu neman takarar da gwaji ya nuna tana shan kwaya.

Ya ce, iya jam’iyyar NNPP ce ta gabatar da masu neman takarar don gwajin shan kwaya a yayin da ake shirin mika sunayen ‘yan takara ga hukumar Zabe ta KANSIE.

Hukumar zaben dai ta sanya ranar 26 ga watan Oktoba don gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar