Home Labarai Zaɓen ƙananan hukumomi na Kano: Kotu ta dakatar da KANSIEC daga karbar N10m kudin fom din takara

Zaɓen ƙananan hukumomi na Kano: Kotu ta dakatar da KANSIEC daga karbar N10m kudin fom din takara

0
Zaɓen ƙananan hukumomi na Kano: Kotu ta dakatar da KANSIEC daga karbar N10m kudin fom din takara

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja, ta dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, KANSIEC, daga karbar Naira Miliyan 10 da Miliyan 5 a matsayin kudin fom din takarar shugaban karamar hukuma da na Kansila a jihar Kano.

Alkalin kotun, mai shari’a Emeka Nwite ne ya bada umarnin a ranar Laraba.

Jam’iyyun APP da ADP da SDP ne dai suka shigar da karar.

Ana karar hukumar zabe mai zaman kanta ne kadai a takardar karar da aka shigar.