Home Labarai Ƙananan hukumomi a Kano sun kai ƙarar shugaban ICPC bisa zargin watsi da umarnin kotu

Ƙananan hukumomi a Kano sun kai ƙarar shugaban ICPC bisa zargin watsi da umarnin kotu

0
Ƙananan hukumomi a Kano sun kai ƙarar shugaban ICPC bisa zargin watsi da umarnin kotu

Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi ta Kasa (ALGON), reshen jihar Kano ta shigar da korafi gaban kwamitin kula da lauyoyi na Kotun Koli akan shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, Musa Aliyu, SAN, bisa zargin ƙin bin umarnin kotu.

Jaridar Guardian ta rawaito cewa a takardar ƙorafin, wacce Barista Shamsi Ubale Jibril ya sanya wa hannu a jiya Talata, ALGON, ta zargi shugaban ICPC da tura jami’an sa suka kutsa gidan shugaban riko na ƙaramar hukumar Rimin-Gado cikin dare, tare da kama shi da kuma tsare shi duk da kotu ta hana hukumar yin hakan.

A takardarJibril ya yi nuni da cewa a ranar 27 ga watan Agusta, babbar kotun juya ta baiwa ICPC da sauran hukumomin yaki da cin hanci da rashawa umarni na kar su kama, ko gayyata ko razana ko tsare wani ɗan kungiyar ALGON, wacce ta shigar da ƙara akan hakan.

Haka zalika, masu korafin sun shigar da kara a kan shugaban na ICPC akan yunkurin kama shugaban ƙaramar hukumar Karaye, inda au ka nemi kotu ta hana duk wani yunkuri na tauye musu ƴancin su na ƴan ƙasa.

ALGON ta yi kirarin cewa an tauye mata hakkin kuma an saba doka ace hukumomin yaƙi da cin-hanci da rashawa da yawa su rika bincikar mambobin ta akan zargin lefi guda daya na zargin badaƙalar kwangilar kawo magunguna zuwa kananan hukumomi.

“Mun rubuta wannan korafi ne bisa abinda mu ke ganin ya saɓa da kwarewa ta aikin lauyanci, musamman ga mutumin da ya kai muƙamin SAN a aikin.

“Duk da cewa kotu ta hana shi kama ko gayyatar wani daga cikin mambobin ALGON, wadanda su mu ke wakilta a kotu, sai gashi, abin mamaki da ban al’ajabi , shugaban ma ICPC a Kano ya ki bin umarnin kotun ta hanyar kamo da razana wadanda mu ke karewa. Wannan bai dace ba ga mai muƙamin SAN kuma ya saɓawa kwarewa ta aikin lauyanci.

“Mu na kira ga wannan kwamiti da ya bincika wannan magana ya kuma ɗauki matakin da ya dace,” in ji takardar korafin.