Home Labarai Waɗanda su ka yi garkuwa da Sarki a Filato sun nemi naira miliyan 500 kuɗin fansa

Waɗanda su ka yi garkuwa da Sarki a Filato sun nemi naira miliyan 500 kuɗin fansa

0
Waɗanda su ka yi garkuwa da Sarki a Filato sun nemi naira miliyan 500 kuɗin fansa

 

Ƴan fashin dajin da su ka yi garkuwa da Sarkin Pyem, Charles Mato Dakat sun nemi a basu naira miliyan 500 a matsayin kuɗin fansa.

Wata majiya a masarautar, ta shaidawa jaridar The Nation cewa ƴan ta’addan sun tuntuɓi masarautar ne ta wayar Sarkin.

“Mun yi magana da su. Mai martaba ne ma ya fara kiran wayar mu ka yi magana da shi.

“Bayan nan suma waɗanda su ka yi garkuwar da shi su ka yi mana magana ta wayar tasa.

“Sun gaya mana cewa su na kula da Mai Martaba kuma ya na cikin koshin lafiya. Sun ce ba su da niyyar su illata shi, kawai dai su abinda su ke so shine a basu naira miliyan 500 sai su sake shi.

“Ba a fi minti biyar a na wayar ba. Amma sun kira ranar Talata kuma iyalin sa sun ce za su bayar da naira miliyan 30. Sun yi alkawarin za su ƙara kira amma har yanzu dai ba su kira ba,” in ji majiyar.