Home Labarai Ɓangarorin da ke gabza yaƙi a Sudan sun amince da ganawa don tsagaita wuta

Ɓangarorin da ke gabza yaƙi a Sudan sun amince da ganawa don tsagaita wuta

0
Ɓangarorin da ke gabza yaƙi a Sudan sun amince da ganawa don tsagaita wuta

Kungiyar haɗin kan ƙasashen gabashin Afirka ta Igad ta ce ɓangarori biyun da ke yaƙi da juna a Sudan za su yi tattaunawar ido da ido domin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce jagororin biyu sun amince a kawo ƙarshen yaƙin ta hanyar tattaunawar diflomasiyya.

Sanarwar ta ce shugaban RSF da aka kira a waya yayin tattaunawar ya ce shi ma ya amince cewa za a iya kawo ƙarshen yaƙin ne ta hanyar zama a tebirin sulhu.

Wakilin BBC ya ce a baya an yi ta ƙoƙarin tattaunawar samar da zaman lafiya amma hakan ya ci tura, wadda aka yi a baya ta shigar da kayan agaji ma ba ta ɗauki wani dogon lokaci ba.

Sama da mutum miliyan shida ne suka rasa muhallansu a Sudan sanadin yaƙin da aka fara tun a watan Afrilu.

BBC Hausa