
Sama da baƙi 40 da suka halarci bikin aure sun kamu da rashin lafiya sakamakon kamuwa da gubar abinci a abincin da su ka ci a lardin Takhar da ke arewacin ƙasar Afganistan, in ji ‘yan sanda a yau Litinin.
Wani jami’i danga rundunar ‘yan sandan lardin, Mubin Safi ya ce lamarin ya faru ne a yayin ɗaurin aure a ƙauyen Takhan Abad da ke gundumar Chah Hab a daren Lahadi.
Safi ya ce a cikin marasa lafiya har da ango da amarya.
Ya kara da cewa an kai mutanen da abin ya shafa asibitin gundumar inda da dama daga cikinsu suka samu kulawa a sashin kula da lafiya na cibiyar.
A cewarsa, an kama mutane uku biyo bayan lamarin sannan kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan gubar abincin da aka samu a gundumar.