Home Ƙasashen waje Angola da Libya sun kere Nijeriya wajen samar da ɗanyen mai – OPEC

Angola da Libya sun kere Nijeriya wajen samar da ɗanyen mai – OPEC

0
Angola da Libya sun kere Nijeriya wajen samar da ɗanyen mai – OPEC

 

Kasashen Angola da Libya sun shiga gaban Nijeriya wajen samar da ɗanyen man a watan Agusta.

Adadin danyen man fetur da Nijeriya ke samarwa ya yi ƙasa zuwa ganga 972,000 a duk rana a cikin watan Agusta, inda hakan ya sanya ƙasashen biyu su ka kere ta, in ji OPEC.

Hakan na kunshe ne a rahoton da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC) ta fitar a cikin watan Satumba.

Wannan ne karon farko a cikin shekaru da dama, da Najeriya ta samar da ganga kasa da miliyan daya ta danyen man fetur a rana.

Kazalika rahoton na OPEC ya ce lamarin ya sa kasashen Angola da Libya sun sauko da Najeriya wurin samar da danyen man fetur a dan tsakanin.

Rahoton ya ce ” fitar da danyen mai ya karu a kasashen Libya da Saudi Arabia, yayin da ya ragu a Najeriya.”