Home Labarai Ƴansanda na neman dan kasar Burtaniya ruwa a jallo bisa zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu

Ƴansanda na neman dan kasar Burtaniya ruwa a jallo bisa zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu

0
Ƴansanda na neman dan kasar Burtaniya ruwa a jallo bisa zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu

Rundunar Ƴansanda ta Ƙasa ta ayyana neman Andrew Wynne wanda aka fi sani da Andrew Povich ko Drew Povey, dan kasar Burtaniya kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu.

Rundunar ta ce ta fara bincike mai zurfi kan wasu ‘yan kasashen waje da suke yunkurin kifar da gwamnatin Dimokuradiyya a Nijeriya.

Daily Trust ta rawaito cewa kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, wanda ya bayyana hakan a shelkwatar ‘yan sanda ta kasa dake Abuja, ya ce dan kasar Burtaniyar ya kama hayar waje a ofishin kungiyar kwadago, sannan ya kafa makaranta domin ya zama ya boye manufarsa.

Rundunar ƴansandan ta ce shaidu sun nuna yadda Andrewa ga dinga bada umarni tare da lura da zanga zangar da aka yi a watan Agusta.

Sannan ƴansandan sun ce, mutumin ya bada tallafin kudade don ganin an kifar da gwamnatin.