Home Labarai Ƴansanda sun cafke mutumin da ya bada cin-hancin miliyan 1 don a saki mai garkuwa da mutane

Ƴansanda sun cafke mutumin da ya bada cin-hancin miliyan 1 don a saki mai garkuwa da mutane

0
Ƴansanda sun cafke mutumin da ya bada cin-hancin miliyan 1 don a saki mai garkuwa da mutane

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani mai suna Bamuwa Umaru, mai shekaru 62 da haihuwa da laifin bayar da cin hancin Naira miliyan 1 domin a sako wani da ake zargi da yin garkuwa da mutane.

Kakakin rundunar ƴansanda a jihar, SP Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano a jiya Talata.

“A ranar 16 ga Disamba, 2022 da misalin karfe 2:00 na rana, Bamuwa Umaru, mazaunin garin Shika a jihar Kaduna, ya tunkari jami’in da ke kula da masu yaki da masu garkuwa da mutane, sashin binciken manyan laifuka na jihar Kano, SP Aliyu Mohammed.

“Wanda ake zargin ya bayar da Naira miliyan 1 a matsayin cin hanci domin a saki wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne, Yusuf Ibrahim, mai shekaru 27 a kauyen Danjibga, jihar Zamfara,” inji shi.

Kiyawa ya ce, tawagar ‘Operation Restore Peace’ ce, karkashin jagorancin CSP Usman Abdullahi, DPO Rijiyar Zaki Division Kano ne su ka kama wanda ake zargin da garkuwa da mutane.

“Wani direban da su ka yi garkuwa da shi a hanyar Funtuwa-Gusau ne ya gano Yusuf Ibrahim, kuma suka karbi kudi naira 500,000 a matsayin kudin fansa kafin a sako shi.

“A binciken farko, Ibrahim ya amsa laifinsa sannan ya kara da cewa da hannun sa a cikin jerin garkuwa da mutane a kauyukan Sheme, Yankara, Faskari da Kucheri dake jihohin Katsina da Zamfara.

“Ibrahim ya kuma yi ikirarin cewa gungunsu sun kashe kusan 10 daga cikin wadanda su ka sace, kuma shi kadai ya kashe biyu daga cikin wadanda aka sace.

“Za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu bayan an kammala bincike,” in ji shi.