
Rundunar ƴansanda ta ƙasa ta yi gargadi kan zuwa da dabbobi, musamman karnuka zuwa rumfunan zabe a ranar zabe.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata a Abuja.
Ya ce zuwa rumfunan zabe da karnuka a ranar zabe ya saba wa tanadin dokar zabe.
A cewar sa, ƴansanda ba za su lamunci irin wannan dabi’a ba domin hakan zai kai ga cin zarafi da kuma tursasa masu zabe.
“Tsarin sashe na 126 (1) na dokar zabe ta 2022, ya bayyana karara irin ayyukan da masu zabe za su yi da waɗanda ba za su yi ba na karya dokar zabe, kuma hukunci ne a karkashin doka.
“Sakin layi na (f) ya ambaci mallakar makamai da aka lissafta don tsoratar da masu zabe da jami’an zabe.
Ya kara da cewa “Karnuka za a iya sanya su a matsayin makamai masu tayar da hankali kamar yadda masu su ko masu kula da su za su iya amfani da su don tsoratarwa, musgunawa da haifar da hari da cutar da jiki ga wasu,” in ji shi.
Adejobi, don haka ya gargadi masu niyyar zuwa da karnukan nasu ko wace irin manufa a rumfunan zabe, da su dakata kada su yi.