Home Labarai Ƴansanda sun kama wasu bisa zargin yunƙurin kai hari a bikin ranar ƴanci a Abuja

Ƴansanda sun kama wasu bisa zargin yunƙurin kai hari a bikin ranar ƴanci a Abuja

0
Ƴansanda sun kama wasu bisa zargin yunƙurin kai hari a bikin ranar ƴanci a Abuja

Jami’an rundunar ƴansandan birnin tarayya Abuja sun kama wasu mutane 4 da ake zargi da shirya kai hari hukumomin gwamnati da rukunin gidaje a ranar bikin ‘yanci.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Alhamis, mai magana da yawun rundunar, Josephine Adeh ta bayyana sunayen waɗanda ake zargin da suka haɗa da Yau Sani wanda aka fi sani da Baba (tsohon wanda kotu ta taba samu da laifi) da Nuhu wanda aka fi sani da Giwa da Kabiru Mohammed da Yusuf Hassan.

Adeh ta ce waɗanda ake zargin sun kuma amsa laifin yin garkuwa da mutane da dama a birnin tarayya Abuja da Kaduna da Niger tare da kashe mutane 7.

Ta ce, “Sashin yaki da garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan Abuja, a ranar 1 ga watan Oktoba, bisa rahotan sirri da ya samu ya bibiya tare da kama kasugurman masu satar mutane wadanda suka addabi birnin tarayya Abuja”.

” Wadanda ake zargin sun amsa laifin yin garkuwa da mutane tare da kisan mutane 7 a Abuja da kewayenta.

Adeh ta ce bayan kama mutanen, sun jagoranci ‘yansanda zuwa dajin da soke boye makamansu.

Ta kara da cewa an kwato bindigogi kirar AK-47 guda 4 da Alburusai 175.