
Akalla mutane takwas ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani sabon rikici da ya barke tsakanin Kutep da Fulani makiyaya a kauyukan Kwe Sati da Fikye dake karamar hukumar Ussa a jihar Taraba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansandan jihar, Abdullahi Usman, wanda ya tabbatar da kisan, ya ce kila adadin wadanda suka mutu ka iya zarce haka.
Yayin da ya ke tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike, kakakin ƴansandan ya ce lamarin na baya-bayan nan ya faru ne a sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin makiyaya da kabilar Kutep.
“An yi rikicin kabilanci tsakanin Kuteps da Fulani. Lamarin ya faru ne a makon da ya gabata, kuma an tabbatar da mutuwar akalla mutane takwas.
“Akwai wani harin da ba zan iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba a halin yanzu saboda ana ci gaba da gudanar da bincike,” in ji Mista Usman.
Kakakin ƴansandan ya kuma bayyana cewa al’amura sun koma daidai kuma mutane sun fara komawa gidajensu.
Sai dai kuma a halin da ake ciki, shugaban karamar hukumar Ussa, Abershi Musa, ya yi murabus daga mukaminsa.
Ya zargi gwamnatin jihar da gaza daukar mataki kan kashe-kashen da ake zargin Fulani makiyaya ne suka yi a yankin Kutep.