
Jami’an ƴansanda a Anambra sun kuɓutar da masu yi wa kasa hidima, NYSC su 15 da a ka yi garkuwa da su, wadanda suka kammala horo a Imo.
Ƴan yiwa ƙasa hidimar sun fito ne daga sansanin horo na NYSC da ke Eziama-Obaire, Ƙaramar Hukumar Nkwerre, Imo, a cikin wata mota a kan hanyarsu ta zuwa Legas sai aka sace su.
DSP Tochukwu Ikenga, jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansanda a jihar Anambra ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata a Awka.
Ya ce jami’an ƴansandan sun amsa kiran gaggawar da aka yi musu a hanyar Isseke, babban titin Ihiala-Orlu da karfe 12:15 na dare, tare da kubutar da ƴan yiwa ƙasa hidima su 15 da aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba.
“Bayanan sun nuna cewa masu yiwa ƙasa hidimar sun kammala ɗaukar horo na tsawon makonni uku a yau kuma suna kan hanyarsu ta zuwa Legas kafin daga bisani wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba suka tare motarsu a mahadar Total a Ihiala a cikin wata farar Toyota Hilux.
“sai su ka karkatar da motar ta masu bautar ƙasa zuwa Isseke, babban titin Ihiala-Orlu inda ƴan bindigar suka yi garkuwa da su.
“Lokacin da ‘yan bindigar suka lura jami’an ‘yan sanda suna bin su, sai suka zubar da ƴan bautar ƙasar sannan suka tsere da motar bas Toyota Hiace mai lamba EPE 353 YE,” inji shi.