Home Labarai Ƴanta’adda sun kashe DPO da ƴansanda 4 a Neja

Ƴanta’adda sun kashe DPO da ƴansanda 4 a Neja

0
Ƴanta’adda sun kashe DPO da ƴansanda 4 a Neja

Rundunar ƴansanda a Neja ta tabbatar da mutuwar wani DPO mai suna SP Mukhtar Sabiu da wasu ƴansanda hudu a wani artabu da ƴan bindiga da su ka yi a Ƙaramar Hukumar Gurara a ranar Asabar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da DSP Wasiu Abiodun, jami’in hulda da jama’a na rundunar, ya fitar a Minna a jiya Lahadi.

“A ranar 11/02/2023 da misalin karfe 1100 ne aka samu labarin cewa an ga wasu ‘yan bindiga dauke da makamai a kusa da kauyukan Kwakuti-Dajigbe da ke cikin garin Lambata, a kokarinsu na kai farmaki kan wasu al’ummomi da ke kewayen karamar hukumar Gurara.

“sai rundunar ƴansanda daga sassan Gawu-Babangida da Paiko, sojoji da ’yan banga su ka danna zuwa wurin.

“’an yi artabu da yan ta’addan, inda aka kashe da dama daga cikin su tare da fatattakar su, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.

“Abin takaici, DPO ɗin Caji-ofis na Paiko, SP Mukhtar Sabiu da wasu ‘yan sanda hudu daga sassan biyu sun rasa rayukansu a yayin fafatawar da aka yi da bindiga.”

Kakakin ya ce daga baya kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogundele Ayodeji ya jagoranci tawagar da suka taimaka wajen gano gawarwakin ma’aikatan da suka mutu.