Home Siyasa Ɗanzago ga Ganduje: Kawai ka bada kai bori ya hau

Ɗanzago ga Ganduje: Kawai ka bada kai bori ya hau

0
Ɗanzago ga Ganduje: Kawai ka bada kai bori ya hau

 

Ahmadu Haruna Zago, Shugaban Jam’iyar APC ɓangaren tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya yi kira ga gwamna Abdullahi Ganduje da ya rungumi ƙaddara a kan rushe shugabannin jam’iyar na ɓangaren sa da kotu ta yi.

A ranar Talata ne dai wata babbar kotu a Abuja ta rushe shugabancin APC na Abdullahi Abbas, inda ta tabbatar da na Ɗanzago.

Da ya ke zantawa da manema labarai a Kano, Ɗanzago ya baiyana cewa dama can Allah Ya rubuta sai ya yi shugabancin APC, inda ya yi kira ga Ganduje da ƴan ɓangaren sa da su bi shugabancin na sa domin nasarar jam’iyar a Kano.

A cewar Ɗanzago, kundin tsarin mulkin ƙasa da kuma dokar ƙasa ce ta ƙwace shugabancin jam’iyar ta bashi.

Ya ƙara da cewa, da ƴan ɓangaren Shekarau, wanda su ka yiwa kan su laƙabi da G-7, da tsagin Ganduje ɗin dukkan su ƴan APC ne, inda ya ce”babu wani gori da za a yi mana. Nima da nake shugaban jam’iya, ɗan jam’iyar ne, ba da ga wata jam’iya na zo ba.”

“Lokacin da mu ke yaƙin neman shugabancin jam’iya gani a ke shirme mu ke. Gani a ke wasan kwaikwayo mu ke yi.

“Sabo da haka ga shi yanzu Allah Ya bani. Ina kira ga Ganduje da sauran ƴan jam’iya da su biyo wannan tafiya domin kada ƙurar ta yi yawa,” in ji Ɗanzago.

Daily Nigerian Hausa