Home Siyasa APC ta ɗage zaɓen fidda-gwani na ƴan takarar shugaban ƙasa

APC ta ɗage zaɓen fidda-gwani na ƴan takarar shugaban ƙasa

0
APC ta ɗage zaɓen fidda-gwani na ƴan takarar shugaban ƙasa

 

 

 

Jam’iyyar APC mai mulki ta ɗage zaɓen fidda-gwani na shugaban kasa.

Jam’iyar dai ta saka ranakun 29 da 30 ga watan Mayu domin gudanar da zaɓen, amma kuma da ga bisani sai ta ɗage.

Barista Felix Morka, sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau Asabar.

Ya ce a yanzu za a gudanar da zaɓen ne tsakanin ranakun 6,7 da 8 ga watan Yunin 2022.

“Biyo bayan tsawaita wa’adin da hukumar zabe mai zaman kanta ta yi na mika sunayen ‘yan takarar jam’iyyun siyasa, jam’iyyar APC ta ɗage babban taronta na musamman na zaben fidda-gwani na shugaban kasa daga ranar Lahadi 29 ga wata zuwa Litinin 30 ga watan Mayu, 2022 zuwa Litinin. 6 ga Laraba, 8 ga Yuni, 2022,” in ji jam’iyyar