Home Siyasa 2023: APC ta amince Kaka Shehu ya maye gurbin Kashim Shettima a Majalisar Dattijai

2023: APC ta amince Kaka Shehu ya maye gurbin Kashim Shettima a Majalisar Dattijai

0
2023: APC ta amince Kaka Shehu ya maye gurbin Kashim Shettima a Majalisar Dattijai

 

 

 

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, sun amince da Kaka Shehu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen Sanatan Borno ta tsakiya.

Gwamna Babagana Zulum me ya bayyana hakan a karshen taron masu ruwa da tsaki a yau Alhamis a Maiduguri.

Ya ce masu ruwa da tsakin sun zaɓi Shehu ne domin ya maye gurbin Sanata Kashim Shettima, wanda aka zaba a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu.

Gwamnan ya bayyana zabin Shehu a matsayin wani abu da Allah ya kaddara, inda ya kara da cewa: “Shehu dan jam’iyya ne na gaske kuma ya cancanci goyon bayan mambobinta.

Har ila yau, Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Ali Dalori ya yaba da wannan ci gaban, inda ya kara da cewa wakilan za su bi ka’idojin da suka dace domin tabbatar da Shehu a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Shehu shi ne kwamishinan shari’a na jihar.

Gundumar Borno ta tsakiya ta kunshi ƙaryar birnin Maiduguri ; Kananan hukumomin Jere, Mafa, Dikwa, Kala-Balge, Gamboru-Ngala da Konduga.