Home Siyasa APC za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya tabbatar da Machina a matsayin ɗan takara

APC za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya tabbatar da Machina a matsayin ɗan takara

0
APC za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya tabbatar da Machina a matsayin ɗan takara

 

 

Har yanzu tsugune ba ta ƙare ba kan makomar takarar Bashir Machina, dan takarar kujerar Sanatan Yobe ta Arewa a jam’iyyar APC, duk da amincewar da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya yi na shan kaye, kuma ya sha alwashin ba zai ɗaukaka kara kan hukuncin ba.

Idan ba a manta ba, wata babbar kotu da ke Damaturu a jihar Yobe ce ta amince da Machina a matsayin ɗan takarar Sanatan Yobe ta Arewa, inda ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC da ta sanya sunansa a jerin sunayen ƴan takara da su ka fitar.

Sai dai jam’iyyar APC, reshen jihar Yobe a wata sanarwa da shugabanta, Mohammed Gadaka ya fitar a yau Juma’a, ta dage cewa shugaban majalisar dattawan ya ci gaba da kasancewa a matsayin ɗan takara a yankin, kamar yadda kwamitin koli na kasa na APC, karkashin jagorancin Abdullahi Adamu, NWC, ya amince da shi.

Gadaka ya bayyana cewa jam’iyyar, reshen jihar za ta daukaka kara kan hukuncin da kotu ta amince da Machina a matsayin dan takarar Sanata na jam’iyyar a yankin .

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Muna sane da cewa ranar Laraba 28 ga Satumba, 2022, hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, ta yanke dangane da zaben Sanatan Yobe ta Arewa da ke tafe.

“Duk da haka, cikin girmamawa mun yi watsi da matakin da Shugaban Majalisar Dattawa, Mai Girma Sanata Ahmad Lawan ya ɗauka na amincewa da hukuncin da kotu ta yanke, wanda ya hana shi tsayawa takara da kuma shiga zaben.

“A bisa ƴancin mu na shari’a, jam’iyyar APC reshen jihar Yobe ta yanke shawarar ɗaukaka kara kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke domin amfanin jihar Yobe, Najeriya da kuma shugabanci na gari.