
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya, Babachir Lawal, ya ce zaɓin da ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahgmed Tinubu ya yi na Musulmi a matsayin mataimakinsa gagarumin kuskure ne.
A ranar Lahadi ne Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a zaben da za a yi a shekara mai zuwa 2023.
Lawal, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu da Kansa a ranar Talata, inda yace daukar wannan matakin kuskure ne babba.
Babachir ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar jiya Talata, inda yake ganin illar hakan kasancewar Tinubun shi ma Musulmi ne.
Tsohon Sakataren Gwamnatin wanda ya mara wa Tinubu baya a zaben fitar da gwani na APC, ya ce zaben na Shettima ya nuna cewa wasu ‘yan baranda kuma ‘yan amshin-shata ne suka takura Tinubun ya yi haka.
Ya ce bisa ga dukkan alamu, gwamnonin arewa da wasu manyan arewar ne suka sa hakan , da cewa ba za su taba zabar dan takarar da ke da mataimaki Kirista dan arewa ba, kuma shi Tinubun ya yarda da su, in ji Babachir.
Ya yi gargadi da cewa, ”Idan har Tinubun yana ganin wannan zabin shi zai ba shi nasarar samun kuri’un Musulmin arewa, to ya yi kuskure.”
”Saboda za su yi tururuwa su zabi daya daga cikin ‘ya’yansu ne, saboda haka al’adarsu take” In ji shi.
”Buhari, wanda shi ne dansu na fari ba zai kasance dan takara ba a 2023. Amma Atiku dansu na biyu zai kasance.” In ji Babachir.
Saboda haka Tsohon Sakataren yana ganin Atiku Abubakar dan takarar babbar jam’iyyar hammaya, PDP, ‘yan arewa za su zaɓa.