Home Siyasa APC ta bada hujjar saka Sanatan PDP a jerin sunayen ƴan kwamitin yaƙin zaɓen Tinubu

APC ta bada hujjar saka Sanatan PDP a jerin sunayen ƴan kwamitin yaƙin zaɓen Tinubu

0
APC ta bada hujjar saka Sanatan PDP a jerin sunayen ƴan kwamitin yaƙin zaɓen Tinubu

 

 

Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka, ya ce ba abin mamaki ba ne da jigo a jam’iyyar PDP kuma sanata mai wakiltar Enugu ta Gabas, Chimaroke Nnamani, ya shiga jerin sunayen kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar.

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa a jiya Juma’a ne sakataren kwamitin, James Faleke, ya fitar da jerin sunayen mambobi 422 na kungiyar yakin neman zaben .

Jerin sunayen ya ƙunshi na ƙusoshin jam’iyya da ‘ya’yan jam’iyyar APC da suka haɗa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ɗaukacin gwamnonin jam’iyyar APC, masu rike da mukamai da tsofaffin ministoci, da wasu mambobin kwamitin ayyuka na kasa, NWC, na jam’iyyar.

Sai dai a wata hira da wakilin DAILY NIGERIAN ta wayar tarho, sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na kasa ya bayyana cewa Nnamani bai shiga jam’iyyar ba APC ba, yana mai cewa jigon na PDP ya bayyana goyon bayansa ne kawai ga halayen shugabancin Bola Tinubu.

“Yakin neman zaben shugaban kasa ba lallai ne ya shafi jam’iyya ba; na masu goyon bayan dan takara ne. Kuma idan kun lura da furucin Chimaroke kwanan nan, kun san yana matukar goyon bayan dan takararmu na shugaban kasa. Ya yi imanin Asiwaju alheri ne, kuma yana da dukkan cancantar da ake buƙata don yin hidima ga mafi girman ofishi na ƙasar,” in ji shi.

Morka ya ce duk da cewa bai samu tabbaci daga dan takarar shugaban kasa ba, goyon bayan da Nnamani ya nuna ga Tinubu na iya zama dalilin shigar da shi cikin majalisar yakin neman zaben.